Ana Wata: An Haramtawa Ma’aikatan Asibitin Tarayya Yin Kirifto (Mining)

best seller i

Hukumar gudanarwar Asibitin Tarayya da ke Jihar Gombe (FTH) ta haramta wa ma’aikatanta yin ‘kirifto’ ko ‘mining’ a lokacin da suke bakin aiki.

Alfijir Labarai ta rawaito hukumar ta ce ta lura harkar ‘mining’ din tana dauke hankalin ma’aikata daga kula da marasa lafiya a lokutan da suke bakin aiki.

Wata sanarwa da aka aike wa ma’aikatan asibitin ta ce suna da damar yin harkokinsu na yau da kullum a lokacin da ba su bakin aiki.

Kamar yadda Adamu Usman Tela, Mataimakin Daraktan Gudanarwa na asibitin ya tabbatar wa Trust Radio, ya ce sun lura da hakan ne tun da wuri suka dauki matakin gaggawa kafin a kawo musu korafi.

“Mun dauki wannan mataki ne tun kafin a fara samun salwantar rayuwa, domin kula da lafiyar al’umma shi ne abu na farko”

Harkar ‘mining’ a ’yan tsakankanin nan dai ta zama ruwan dare tsakanin al’umma maza da mata, ciki har da ma’aikata masu daukar albashi.

Daily trust

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *