Kotu Ta Saka Ranar Yanke Hukunci Kan Dambawar Masarautar Kano

CJ kano

Babbar Mai Shari’a ta jihar Kano, Dije Abdu Aboki ta sanya ranar 12 ga watan Oktoba a matsayin ranar yanke hukunci kan karar da gwamnatin jihar Kano ta shigar na dakatar da Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero daga gyaran fadar Nassarawa.

Gwamnatin, ta hannun lauyan ta, Rilwanu Umar (SAN), ce ta shigar da karar a ranar 12 ga watan Satumba, kuma Bayero ne kaɗai aka shigar da ƙarar a kansa.

Kotun, a ranar 13 ga Satumba ta hana Sarkin yin wani gini ko gyara a fadar gidan Nassarawa.

Daga nan sai kotun ta bada umarnin dakatawa da komai har sai bayan sauraron ƙarar.

Daily Trust

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *