Ana Kukan Targade! Kungiyar Ma’aikatan Jinya Da Ungozoma Na Shirin Tsunduma Yajin Aiki A Kano

lafiya

Kungiyar ma’aikatan jinya da ungozoma ta kasa (NANNM) reshen jihar Kano, ta bai wa gwamnatin jihar wa’adin kwanaki 15 da ta gaggauta biya musu bukatunsu ko kuma ta tsunduma yajin aikin a fadin jihar.

Alfijir labarai ta rawaito hakan na kunshe ne cikin wata wasika mai dauke da sa hannun mukaddashin sakataren kungiyar kuma jami’in hulda da jama’a na kungiyar a yau laraba, Kwamared Ahmad Hazmat Sharada, kan biyan wasu bukatu da ba a warware ba tsakanin ma’aikatan jinya da gwamnatin jihar tun daga watan Disambar 2023.

A cikin wasikar mai dauke da kwanan watan 2 ga watan Oktoba kuma aka aika wa shugaban ma’aikatan jihar Kano, NANNM, ta yi gargadin cewa, ma’aikatan jinya da ungozoma a fadin jihar za su janye ayyukansu daga dukkan cibiyoyin kiwon lafiya da cibiyoyin horo idan gwamnati ta gaza biya musu bukatunsu.

Wasu daga cikin buƙatun da aka zayyana a cikin wasiƙar sun haɗa da biyan kudaden alawus ɗin haɗari ga ma’aikatan jinya, da inganta tsarin aikin ma’aikatan jinya.

Kungiyar ta kuma bukaci a biya kashi 25 cikin 100 na tsarin biyan albashi na CONHESS, tare da wasu bukatu da aka zayyana a cikin wata tunatarwa da aka aika wa gwamnati a ranar 20 ga Agusta, 2024.

Wasikar ta kuma yi nuni da kokarin da kungiyar ta yi na tsinkayar da gwamnatin jihar ta hanyar aika wasiku, amma ba wata gamsasshiyar amsa har ya zuwa yau.

Idan har yajin aikin ya tabbata, zai iya haifar da mummunan sakamako ga tsarin kiwon lafiya na jihar saboda janye ayyukan jinya na iya haifar da dakatar da ayyuka masu mahimmanci na asibiti, lamarin da zai shafa marasa lafiya da dama a fadin jihar Kano.

Har yanzu gwamnatin jihar Kano ba ta mayar da martani kan wa’adin da NANNM ta yi ba har zuwa lokacin hada wannan rahoto.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *