Kwamishiniyar Mata Da Walwala Ta Gwangwaje Masu Larurar Laka Da Kayan Amfaninsu Tare Da Kuɗi A Kano

Aisha Saji

Daga Rabi’u Usman

Kwamishiniyar Mata da walwala karkashin jagorancin gwamnatin kano ta bayar da tallafin kayayyakin kula da kiwon lafiya ga masu larurar laka tare da  tallafin kudi naira miliyan 1 domin gudanar da bikin zagayowar ranar masu larurar laka ta duniya.

Alfijir labarai ta rawaito Kwamishinar ma’aikatar mata, kananan yara da masu bukata ta musamman Haj Aisha Lawan saji rano ce ta raba kayayyakin ga Kungiyar a shalkwatar ma’aikatar mata kananan yara da masu bukata ta musamman da yammacin ranar Alhamis.

Kayayyakin da aka bayar sun hadar da keken zama (Wheel chair) guda 20, audugar mata, man tsabtace hannu, katata, bandeji da kayan dressing harma da zunzurutun kudi naira miliyan 1, da dai sauran su.

Bayan kammala taron ne wakilin mu ya zanta da kwamishinar akan yanda aka gudanar da rabon kayan jin kan.

Inda ta bayyana cewar, mai Girma gwamnan kano Abba Kabir Yusuf ya sahale wa ma’aikatar ne domin mata, kananan yara da masu bukata ta musamman suma susan gwamnatin kano tana damawa da su.

Ta kara cewar, mutane da yawa musamman masu bukata ta musamman da masu larurar laka suna zuwa ma’aikatar dokin kawo koken su na rashin irin wadannan kayayyakin na amfanin yau da kullum.

Don haka gwamnan ya bayar da umarnin a samar musu da abinda ya sawwaka domin a rage musu radadin damunar su.

A nasu bangaren Wasu daga cikin mutanen da suka amfana da tallafin musamman shugabancin Kungiyar masu bukata ta musamman bangaren masu larurar laka, sun bayyana Jin Dadin su sakamakon yanda suka ce sun dade suna neman mai share musu hawaye akan damuwar su tare da neman wadannan kayayyakin amma basu da kudin siya.

Sai gashi rana tsaka gwamnatin kano ta biya musu bukatun su Wanda suka dade suna nema.

A karshe sunce nan da 1 ga watan December zasu gudanar da bikin zagayowar ranar masu larurar laka wanda majalisar Dinkin Duniya take warewa sannan su baiwa mambobin Kungiyar musamman wadanda suke da bukatar kayayyakin.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *