Rundunar ‘Yansandan Jihar Ogun ta kama Ogunlana Yemisi mai shekaru 28 bisa zargin kaiwa mijinta, Idowu Adebowale, hari da yanke masa al’aurarsa da wani abu mai kaifi yayin rashin jituwa da ta faru tsakaninsu.
Alfijir labarai ta rawaito lamarin ya faru ne a ranar 15 ga Oktoba, 2024, da misalin karfe 4:30 na safe.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ‘yansandan Jihar Ogun, SP Omolola Odutola, ta fitar a ranar Litinin.
Odutola ya ce Adebowale, mai shekaru 31, ya kai rahoton harin ga ‘yansanda a ranar Litinin, 21 ga Oktoba, yana nuna wa jami’an ‘yan sanda yankan da aka yi masa a gabobin jikinsa wanda ya ce matarsa ce ta yi masa.
Jami’an bincike sun ziyarci wurin da lamarin ya faru ba tare da bata lokaci ba, kuma an kama Yemisi.
Sanarwar ta ce, “Matar ta musanta zargin yayin da ake yi mata tambayoyi, amma ganin girman raunin da kuma tsawon lokacin da wanda abin ya shafa bai nemi taimakon likita ba, an ba shi fom din likita tare da shawarar ya garzaya asibiti.
“A halin yanzu, wadda ake zargin tana tsare, kuma za a tura lamarin zuwa sashin binciken manyan laifuka a Abeokuta don ci gaba da bincike.
“Wannan batu za a gudanar da cikakken bincike a kai, domin ya kasance lamari ne mai alaka da fushin da ba a iya sarrafa shi, wanda ya haifar da rikicin gida,” in ji Odutola.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj