Wata likitar ido da ke Cibiyar kula da lafiyar Ido ta Ƙasa a Jihar Kaduna, Ganiyat Popoola, wacce ƴan bindiga su ka sace a watan Disamban 2023, ta shaƙi iskar ƴanci daga hannun masu garkuwa da ita bayan ta kwashe watanni 10 a hannun su.
Alrijir labarai ta rawaito an sace ta tare da mijinta, Nurudeen Popoola, wanda soja ne, da kuma ɗan’uwanta, Folaranmi Abdul-Mugni, wanda ya ke zaune tare da su.
Masu garkuwan sun buƙaci kuɗin fansa har naira miliyan 40, wanda aka biya, kuma hakan ya sa suka sako mijinta a ranar 8 ga Maris, 2024, amma suka ƙi sakin Dr Popoola da kuma ɗan’uwan na ta.
A ƙarshe dai, an saki Dr Popoola da ɗan’uwanta a yammacin jiya Laraba, lamarin da ya kawo ƙarshen tsananin wahalar da suka fuskanta a hannun masu garkuwan.
Shugaban Ƙungiyar Likitoci masu neman kwarewa na Najeriya, Dr Tope Osundara, ya nuna farin ciki da shauƙi mai yawa game da sakin ta, inda ya gode wa duk wanda ya ba da gudunmawa wajen tabbatar da dawowar su lafiya.
Domin kasancewa da mu a shafukan sada zumunta za a iya bibbiyarmu ta wadannan
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj