Da Dumi Duminsa! An haramtawa mata shiga kasuwar waya ta Farm Center a wani lokaci

Farm Center

Muna Kira ga Hukumar Hisba ta Jihar Kano data taimakawa kudirin gyaran tarbiyya da kawar da badala a Kasuwar waya ta farm center Dan Magance zuwan Mata bayan karfe 6

Alfijir labarai ta rawaito shugaban gidauniyar Tallafawa Mabukata Daga Tushe wato Grassroot Care and Aid Foundation Amb Auwalu Muhd Danlarabawa ne yayi wannan kira ga rundunar Hisba ta Jihar Kano akan itama ta shigo cikin wannan al’amari Dan bada gudunmawa a dakile abinda kungiyar Kasuwar take kuka akanshi na kawo ko barin Mata a Kasuwar bayan karfe shiga na yamma.

Mun tabbatar da cewar duk abinda akayi kuka akanshi irin wannan to da alama ya dade yana faruwa, kuma yana damun mutanen kirki dake cikin wannan kasuwa, hakan yasa suka sanyawa kansu dokar a hana zuwan matan a wannan lokaci sannan wanda suke ciki su fita Idan lokaci yayi suna cikin kasuwar.

Kasuwa dai kowa yasan wajen sana’a ne ba wajen sharholiya da Mata ba, idan akayi duba ga yawancin Yan wannan kasuwa Matasa ne masu kananan shekaru, wanda rayuwar su tana bukatar kulawa akan bangaren da ya shafi hani da mummuna da kuma umarni da kyakkyawa dan rayuwar ta inganta Kar a barsu su fada halaka.

Muna fatan ita ma kungiyar Kasuwar ta farm center zata hada Kai da rundunar Hisba Dan yin Aiki tare a wannan mataki da shugabanci ya dauka karkashin Amb Jamilu Bala Gama.

Allah ya bada nasara, kuma a cigaba da duba duk wani Abu da aka gani zai cutar da rayuwa ko jefa Yan wannan kasuwa ga halaka da janyo balai ga Kasuwar.

Amb Auwalu Muhd Danlarabawa
Amb Jamilu Bala Gama

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *