Sheikh Abdallah Gadon-Kaya ya magantu akan dan damfarar dake amfani da sunansa

FB IMG 1732740237550

Sheikh Abdallah Gadon Kaya ya baiyana cewa shi ma kusan shekaru biyu ya kwashe ya na neman Aminu Abdullahi, mutumin da ƴansanda su ka kama shi bisa zargin damfarar ƴan kasuwa a jihar Kano.

Alfijir Labarai ta rawaito rundunar ƴansandan jihar Kano a yau Laraba ta sanar da cafke Abdullahi, mai shekaru 50 da haihuwa bisa zargin amfani da sunan Sheikh Abdallah ya cuci al’umma.

Kakakin rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce an kama shi ne bisa korafe-korafen da wajen mutane 20 suka kawo cewa ya sayi kayan su amma bai tura musu kudin ta banki ba, inda ya ke ce musu zai aiko kuɗin an jima kuma shi ƙanin Sheikh Abdallah ne, don haka kar su damu.

Sai dai shi ma Sheikh Abdallah, a hirar da ya yi da Freedom Radio ya nuna takaicin yadda mutumin ke amfani da sunan sa ya na damfarar al’umma.

A cewar Sheikh Abdallah, mutane da dama sun zo wajen sa don bin bahasin kuɗaɗen su na kayan da su ka ce mutumin ya saya da sunan sa, inda malamin ya kara da cewa shi ba ya cim bashi kuma ba wani kaya da yanke siya bashi.

Sheikh Abdallah ya kuma yabawa rundunar ƴansanda bisa kamo mutumin, inda ya kuma yi kira ga al’umma, musamman ƴan kasuwa da su kiyaye kuma su dena yadda ana amfani da sunan sa wajen damfarar su.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *