Mutumin, mai suna Aminu Abdullahi, ya shiga hannu ne bayan da wani dan kasuwa ya kai rahoton cewa ya je shagon sa ya sayi taliya kayan biyu amma sai ya ƙi tura masa kudin akan cewa shi ƙanin Sheikh Abdallah Gadon Kaya kuma zai tura kudin daga baya.
A sanarwar da Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar a yau Laraba, ya ce wanda ake zargin, dan shekara 50 mazaunin Kofar Nassarawa ya dade yana tafka wannan laifi.
A cewar SP Kiyawa, an samu korafi daga sama da mutane 20 akan cutar da yanke musu, inda ya kara da ruwa hakan ce ta sanya rundunar ta dukufa neman sa har kuma ta kama shi.
Ya yi bayanin cewa idan ya karbi Kayan mutane, sai ya yi kamar ya tura musu amma daga bisani sai ya ce musu sai zuwa anjima kuma shi ƙanin Sheikh Abdallah ne saboda haka a ina zan kawo kudi daga bisani kuma sai ya tsere.
SP Kiyawa ya baiyana cewa za a gurfanar da wanda ake zargin idan an kammala bincike.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj