DaDumi-Duminsa: Jami’an tsaro sun kewaye gidan Sarkin Kano Sanusi tare da hana shige da fice

FB IMG 1733479853468

A yau safiyar Juma’a an tashi da ganin jami’an ƴansanda ɗauke da makamai tare da na SSS sun yi ƙawanya a Masarautar Kano, inda Sarki Muhammadu Sanusi ll ke zaune.

Alfijir Labarai ta tattaro cewa jami’an tsaron sun hana shige da fice a gidan Sarkin.

Rahotanni sun baiyana cewa a yau din ake sa ran Sarki Sanusi zai raka sabon Wamban Kano, Munir Sanusi zuwa Bichi, inda zai yi hamkimci.

DAILY NIGERIAN ta jiyo cewa can ma fadar harkokin na Bichi an zuba jami’an tsaro, mai yiwuwa da nufin hana zuwan sabon Wamban.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *