Wata Sabuwa! Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɓullar COVID-19 a ƙasashe 29

COVID 19

Al’umma sun shiga fargaba sakamakon wata sanarwa da Gwamnatin Tarayya ta Ma’aikatar Lafiya ta fitar, inda ta yi kira ga hukumomin kiwon lafiya da su faɗaɗa hanyoyin faɗakar da al’umma game da sake ɓullar sabuwar cutar XEC COVID-19 da ke yaɗuwa a duniya.

XEC shi ne saboda nau’in reshen COVID da ake nazari a kai yayin da COVID-19 ke ƙara sauya salo.

An tabbatar da lamarin ne a karon fari, a ƙasar Australia inda daga baya kuma aka gano cewa a ƙasashe 29 ne.

Sakataren Ma’aikatar, Dakta O.N. Onuma ya bayyana hakan cikin wata takarda inda ya buƙaci al’umma da suka kasance masu kula da kuma ɗaukar mataki.

Ya ce akwai buƙatar a riƙa sanar da duk wani alamun da aka gani na cutar a kowane yanki na ƙasa don kare bazuwar ta.

A watan Satumba ne jaridar ‘News Point Nigeria’ ta ruwaito cewa an samu ɓullar XEC a ƙasashe 27 ciki har da Faransa da Amurka inda mutane 600 suka kamu da ita.

Daga nan ne aka yi ta samun batutuwarta a Birtaniya da Amurka da Denmark da wasu ƙasashen, don haka ne jami’an lafiya ke kira da a ɗauki matakan kariya na kaucewa yaɗuwar cutar.

Manhaja blueprint

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *