Daga Aminu Bala Madobi
Shugaba Bola Tinubu ya amince da shekarun ritaya ga likitoci da sauran ma’aikatan kiwon lafiya daga shekaru 60 zuwa 65.
Dakta Mannir Bature, Sakataren Yada Labarai na Kungiyar Likitocin Najeriya, NMA, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba a Legas.
Bature ya ce an umurci ministan lafiya da walwalar jama’a, Farfesa Muhammad Pate da ya gabatar da amincewar shekarun ritayar a hukumance.
Ya ce Pate ne ya gabatar da wannan sauyin manufofin a lokacin wani babban taro da shugaban NMA, Farfesa Bala Audu, da masu ruwa da tsaki a fannin lafiya.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ