Daga Aminu Bala Madobi
Gwamnan Babban Bankin Najeriya, Olayemi Cardoso na fuskantar kakkausar suka kan zargin biyan wasu ‘yan mata biyu zunzurutun kudi har Naira miliyan 85 duk wata tare da ba su iko fiye da mataimakan gwamnonin bankin.
A ranar 22 ga watan Satumban 2023 ne Cardoso ya hau kujerar gwamnan CBN bayan da aka kori Godwin Emefiele bisa zargin almubazzaranci da kuma cin hanci da rashawa.
Kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito, wasu majiyoyi sun ce matan sun zo tare da shi Sai dai wasu majiyoyi sun ce bayan kwanaki ne kawai matan suka shiga harabar hukumar, wanda hakan ya haifar da shakku da cece-kuce a kan dangantakarsu da gwamnan, wadanda ake biyan su makudan kudade duk wata.
Matan da aketa cece-kuce sun hada da Nkiru Balonwu, wanda ta kafa kamfanin Mai suna The Africa Soft Power Group, dakuma Daphne Dafinome, wata kwararriyar akawu kuma babbar jami’ar gudanarwa na Crowe Dafinone, wani kamfani a Najeriya.
Daraktoci a CBN sun ce Mista Cardoso ya dauki matan ne a matsayin masu ba da shawara ba bisa ka’ida ba, ba tare da bin ka’idojin da aka gindaya ba.
Misali, sun nemi a dauki Ms Balonwu a matsayin mai ba da shawara kan harkokin sadarwa a yayin da CBN ke da cikakken bayani, inganci, kuma ma’aikatan sashen sadarwa na kamfani wanda darakta ke jagoranta kuma aka dora wa alhakin tabbatar da ingancin sadarwa na ciki da waje.
A wani bangaren kuma, masu lura da al’amura sun ce ba a fayyace rawar da uwargida Dafinone ke takawa ba a fili; kawai ta dauki duk wani nauyi da Mista Cardoso ya dora mata.
A kwanakin baya ne gwamnan ya dora matan alhakin tsarawa da aiwatar da wasu shirye shiryeblamarin da janyo cece-kuce domin suna Karban akalla adadin kudaden biyan ma’aikata akalla 1,000 albashin ma’aikata wanda bankin abaya bayannan aka rawaito ya kora.
Rahotonni sunce bankin CBN na da mataimakan gwamnoni hudu: Emem Usoro (Corporate Services Directorate), Muhammad Dattijo (Directorate Policy Economic Directorate), Philip Ikeazor (Financial System Stability Directorate), da Bala Bello (Operations Directorate). Sai dai a halin yanzu ma’aikatan na yin kallon Ms Balonwu da Dafinone a matsayin mataimakan gwamnoni na biyar da na shida a bankin.
Wani ma’aikacin banki ya tabbatar da ikirarin daraktan, inda ya ce ya taba jin daya daga cikin matan na fadin cewa “idan ta zana layi a bankin, ko gwamnan bazai kuskura ya tsallaka ba”.
Ma’aikatan sun kuma zargi Mista Cardoso da biyan matan albashin da ya wuce kaida. Misali, Ms Balonwu, a cewarsu, tana karban Naira miliyan 50 a kowane wata, inda take samun fiye da na gwamna da mataimakan gwamnoni.
Har ila yau albashin nata na kokarin yin kankankan da wajen biyan albashin daraktoci 15, wadanda ke samun kasa da Naira miliyan 3 duk wata.
A nata bangaren, Dafinone na samun Naira miliyan 35 duk wata, wanda aka ce ya haura adadin albashin darakta 10.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp 👇👇
https://chat.whatsapp.com/FNMJaJ3I8Sc0bkkm8aJQbQ