Daga Aminu Bala Madobi
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya umarci dukkan ministocin gwamnatinsa da su bayar rahotonnin ayyukan da suka gabatar ga ‘yan Najeriya.
Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a na kasa Mohammed Idris malagi ne ya sanar da hakan a wani taron manema labarai a Abuja ranar Talata.
Ministan ya ce bayanin da ministocin suka yi shi ne don baiwa ‘yan Najeriya damar sanin abubuwan da gwamnati ta yi da kuma yin tambayoyi.
Rahotonni sunce akwai ministoci 48 a majalisar ministocin Tinubu. Daga cikin su akwai Nyesom Wike, ministan babban birnin tarayya; Adebayo Adelabu, ministan wutar lantarki; David Umahi, ministan ayyuka, Olubunmi Tunji-Ojo, ministan cikin gida, da dai sauransu.
Zamu cigaba da kawo cikakkun rahotonni gaba kadan
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ