Gidauniyar Lamidon Katsina ta kammala rabon goron Sallah na gida-gida da ta saba yi duk shekara a garin Tsauri

FB IMG 1743593767056

A ranar Talata 01/04/2025, gidauniyar a karkashin jagorancin shugaban ta Dr. Aminu Salisu Tsauri ta kammala rabon goron sallah da ta fara gudanarwa kwanaki ukku da suka gabata.

Gidauniyar ta raba buhunnan shinkafa mai nauyin kilo 50kg sama da guda 389 wanda kudin ta suka tasan mai sama da Nairai Miliyan Talatin da kuma kudi Niara dubu biyar ga gidaje 1,202 dake cikin garin na Tsauri.

Da yake gabatar da jawabin sa a yayin kammala rabon kayan goron sallah a madadin Lamidon Katsina Dr. Aminu Salisu Tsauri ya bayyana cewar Alh. Jabiru Salisu Abdullahi Tsauri yace na mika godiya ga al’ummar garin Tsauri da fatan anyi sallah lafiya.

Ya cigaba da cewa wannan abun da aka gudanar somin tabi ne dan Hon. Jabiru Tsauri yana mai tabbatar maku da cewa azumin da zaizo na shekara mai zuwa a garin Tsauri babu wanda zai jira Nepa ko Janareto akwai ayyukan da zaizo da su da yadda Allah idan abun ya tabbata kuma kowa zaije gaba ya bada labari.

Shima da yake gabatar da nashi jawabin zababben shugaban karamar hukumar Kurfi Hon. Babangida Abdullahi ya bayyana cewa Hon. Jabiru Salisu Abdullahi Tsauri abubuwan da yake yi da wannan gidauniyar abu ya kai inda ya kamata ya kai.

Ya kara da cewa duk mai gidancin da yaga bai amfana da wannan tallafi ba a yanzu to ya sani kila lokacin da aka dauki bayanai mutanen gari kila bai da mata amma insha Allahu shekara mai zuwa zai kasance a cikin wannan rabon tallafi.

Daga karshe yayi kira ga matasan karamar hukumar Kurfi da su zama masu bada gudunmuwa wajen ganin an tabbatar da tsaro a karamar hukumar sannan su guje bada bayanan sirri ga yan bindigar daji.

Tun da farko da yake gabatr da jawabin Maraba mai garin Tsauri Magaji Tsauri ya bayyana cewar mu a matsayin mu na shugabanni duk wanda zai taimaki al’ummar mu ko wanene kuma ko daga ina yake muna tare da shi zamu goya mashi baya tare da yi mashi addu’a kuma duk inda ya kamata mu taimake shi zamu tai maka mashi.

Dan haka a madadin al’ummar garin Tsauri muna godiya tare da addu’ar karin samun cigaba ga Hon. Jabiru Salisu Abdullahi Tsauri wannan aiki dama ya saba yi mana a wannan gari.

Mutane da dama ne suka tofa albarkacin bakin su a wajen taron daga cikin su akwai zababben shugaban karamar hukumar Rimi Hon. Muhammad Ali Rimi, da takwaran sa na karamar hukumar Batagarawa sunyi addu’o’i da fatan alkhairi ga Hon. Jabiru Salisu Abdullahi Tsauri akan tunawa da mahaifar shi da yayi.

Taron ya samu halartar Sakataren karamar hukumar Kurfi Hon. Mustapha, Sakataren hukumar ilimin bai daya na jiha da dai sauran al’umma maza da mata.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *