Gwamnatin jihar Jigawa ta ce za ta bullo da shirin bada magani kyauta ga masu cutar siga da hawan jini da kuma sikila.
Alfijir Labarai ta ruwaito kwamishinan lafiya na jihar, Dr Abdullahi Muhammad Kainuwa ya bayyana haka ga manema labarai a Dutse.
Yace tuni gwamna Umar Namadi ya bada umarnin gabatar masa da wannan kudiri domin aiwatar da shirin don kula da lafiyar al’ummar jihar musamman masu karamin karfi.
Dr Abdullahi Kainuwa yana mai cewar a yanzu haka gwamnatin jihar tana gudanar da aikin Dandamalin sabon asibitin kashi na garin Gumel kan naira miliyan 380.
A cewar sa, za a bada kwangilar sayen kayayyakin asibitin Kashi na naira miliyan dari shida.
Kwamishinan ya kara da cewar gwamnatin jihar ta kammala aikin gina dakunan wankin Koda a manyan asibitocin Dutse da Ringim da kuma Kazaure.
Yana mai cewar za a bada kwangilar sayo kayayyakin aikin dakunan domin fara wankin koda kyauta ga al’umma kafin karshen shekarar nan da muke ciki.
Dr Kainuwa, yace a yanzu haka ana wankin koda kyauta a asibitocin garuruwan Gumel da kuma Hadejia.
RN
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD