Gwamnatin Najeriya ta baiwa WAEC da NECO sabon umarni

IMG 20250428 215832

Gwamnatin Najeriya ta umarci hukumar shirya jarabawar yammacin Afirka (WAEC) da kuma hukumar shirya jarabawa ta kasa NECO su koma yin amfani da na’ura mai kwakwalwa (CBT) don gudanar jarrabawar daga watan Mayu/Yuni 2026.

Ministan Ilimi, Dakta Tunji Alausa ne ya bayyana hakan a lokacin da yake sa ido kan jarabawar da jami’an hukumar shirya jarabawar shiga jami’a ta JAMB ke gudanarwa a Bwari, Abuja, ranar Litinin.

Alausa ya bayyana cewa WAEC da NECO za su fara gudanar da aikinsu ta hanyar amfani da CBT daga watan Nuwamba, kuma za a fara ne a lokacin jarrabawar Mayu/Yuni 2026.

“Idan JAMB ta samu nasarar gudanar da jarabawar CBT ga dalibai sama da miliyan 2.2, WAEC da NECO ma za su iya yin haka.

Ya kuma jaddada kudirin gwamnati na sauya tsarin rubutu jarrabawar ta CBT gaba daya, yana mai cewa a jarrabawar WAEC na Mayu/Yuni 2026 za ta zama cikakkiyar jarrabawa ta Kwamfuta.

Karin karatu: 2025: JAMB ta fara UTME na masu bukata ta musamman, ta bayyana nasarorin da cibiyar Kano ta samu

Ministan ya kuma bayyana cewa an kafa wani kwamiti da zai duba ma’aunin jarrabawa a fadin kasar.

Ya yi nuni da cewa, ana sa ran gabatar da shawarwarin kwamitin nazari a wata mai zuwa, wanda ke nuni da cewa an kara yin garambawul a fannin ilimi.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *