Daga Aminu Bala Madobi
Wasu mata da dama a jihar Rivers sun gudanar da wani tattaki a yayin wani taron tallafawa mata wanda cibiyar EUI da ke Fatakwal, karkashin Theresa, uwargidan Gwamnan Rikon Kwarya, Vice Admiral Ibok-Ete Ekwe Ibas (Mai Ritaya) lokacin da ta fara jawabinta.
Gangamin wanda aka ce an gabatar da kayayyakin tallafi ga mata 500 a jihar, ya rikide zuwa rudani lokacin da aka gayyaci uwargidan Gwamnan Rikon Kwaryar, Misis Theresa Ibas, domin ta yi jawabi a madadin uwargidan shugaban kasar. Lokacin da aka bayyana sunanta.
“An gaya mana cewa Uwargidan Shugaban Najeriya za ta zo nan, idan ba ita ba ce, to uwargidan Gwamnan mu, Lady Valerie Sim-Fubara, ce zatayi mana jawabi, ba mai wakiltar wanda ba ya wakiltarmu ba,” daya daga cikin matan a fusace take jawabi awata zanga-zanga da ta rikide
Duk kokarin da masu shirya taron suka yi na kwantar da hankulan jama’a, taron matan sun dage kan bukatarsu inda daga karshe suka fice daga wurin taron baki daya.
Wasu daga cikin matan sun ce ana kallon zanga-zangar a matsayin kin amincewa da tsarin nada Shugaban Rikon Kwarya a jihar Ribas da kuma nuna goyon bayansu ga gwamna Siminalayi Fubara wanda aka dakatar.
A wata hira da aka yi da ita, daya daga cikin matan Ekpeye Favour, ta bayyana abin da ya faru a wajen taron, inda ta ce hakan nuni ne na goyon bayansu da kuma kaunarsu ga gwamnan da aka dakatar
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD