Kungiyar Kwadago Ta Bukaci Tinubu Ya kara Mafi Karancin Albashi Sama da N70,000

IMG 002323 08925 1757287432528

Kungiyar Kwadago ta Ƙasa (NLC) da ma’aikatan gwamnati sun bukaci gwamnati ta sake duba mafi ƙarancin albashi, suna mai cewa N70,000 da ake biya a yanzu ba zai iya ɗaukar nauyin ma’aikata ba.

Sakataren riko na NLC, Benson Upah, ya ce hauhawar farashin kayayyaki, tsadar sufuri, haya da wutar lantarki sun sa albashin ya ragu sosai, inda ma’aikata ke shiga cikin kuncin rayuwa.

Ya gargadi cewa idan gwamnati ba ta ɗauki mataki ba, matsalar za ta tsananta.

Shugaban Ƙungiyar Manyan Ma’aikatan Gwamnati (ASCSN), Shehu Mohammed, ya ce ƙungiyarsu ta nemi a ɗora mafi ƙarancin albashi kan N250,000, domin N70,000 ba zai iya biyan bukatun ma’aikaci da iyalinsa ba.

Rahotanni sun nuna cewa wasu jihohi sun riga sun ɗaga mafi ƙarancin albashi sama da na ƙasa: Imo (N104,000), Legas da Rivers (N85,000), Bayelsa, Niger, Enugu da Akwa Ibom (N80,000), yayin da Ogun, Delta, Benue, Osun da Ondo suma suka ɗaga fiye da N70,000.

Wasu ma’aikata sun ce albashin da suke samu ba ya isa biyan haya, kuɗin makaranta da abinci, suna mai cewa gwamnati ta ɗaga albashi zuwa akalla N150,000 domin farfaɗo da tattalin arziki da inganta jin daɗin ma’aikata.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *