Matatar Mai Ta Dangote Dawo Da Tsarin Sayar Da Fetur Da Naira

IMG 085852 27925 1758959940572

Kimanin ƙasa da sa’o’i 24 da dakatar da tsarin sayar da man fetur a farashin Naira, Matatar Dangote ta janye wannan kudiri.

Matatar ta ɗauki wannan matakin biyo bayan tsoma baki da shugaban kwamitin sayar da ɗanyen mai da Naira ga matatun cikin gida, Dr. Zacch Adedeji, wanda kuma shi ne Shugaban Hukumar Kula da Haraji ta Ƙasa (FIRS) ya yi a ranar Asabar.

Tsarin wanda gwamnatin tarayya ta kafa ta hannun NNPCL yana bai wa matatun cikin gida damar samun ɗanyen mai ta hanyar biyan kuɗi da Naira, domin rage dogaro da dala da kuma tabbatar da wadatar mai a ƙasar.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *