Kungiyar ASUU ta baiwa gwamnatin Najeriya wa’adin makwanci biyu domin warware abinda ke tsakanin su ko su tsunduma yajin aiki
Kungiyar ta ASUU ta ce ta cimma matsayin hakanne ayayin taron majalisar zartaswa na kasa da ta gudanar a ranar Lahadi da ta gabata a jami’ar Abuja.
Shugaban Kungiyar ASUU na Kasa Farfesa Chris Piwuna ya bayyana hakan a wata kwafin takarda mai taken matakin Yajin aiki wadda ya rattabawa hannu.
A cewar shugaban Kungiyar ta ASUU gwamnatin tarayya ta yi watsi da tsarin karatun Jami’oi da kuma yadda gwamnatin ta ke kin ba da kulawa ga bukatun malaman Jami’a a kasar nan.
Kungiyar ta ce akan haka ne ta bawa gwamnatin tarayya wa’adin makonni biyu domin ta warware dukkan batutuwan da ke a tsakaninta da ASUU.
Sanarwar ta ce bayan cikar wa’adin na makonni biyu ba tare da daukar wani mataki ba, Kungiyar ASUU za ta zama ba ta da wani zabi da ya fice ta tsindima yajin aikin gargadi na makonni biyu, wanda daga shi ne kuma za a fara na sai Baba-ta-gani.
Idan ba a manta ba gwamnatin tarayya ta kafa kwamiti ta hannun ma’aikatar ilimi a bisa Jagorancin Babban Sakataren ma’aikatar Abel Enitan domin duba bukatun Kungiyar ASUU a kokarin tabbatar da dorewar karatun Dalibai a Jami’oin Nigeria.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t