Hukumar Custom Data NDLEA Sun Kama Haramtattun Tarin Kwayoyi A Kano

FB IMG 1759474551167

Hukumar Hana Fasa-Kwauri ta Ƙasa (Customs) Shiyyar Kano/Jigawa ta samu nasarar kama miyagun kwayoyi da suka hadar da kwayoyin Pregabalin 261,750 da kuma na tramadol 28,700.

Da yake karin haske kan lamarin a Ofishin Hukumar dake kan Titin Sani Marshall dake cikin Birnin Kano, Kwaturolan Hukumar Hana Fasa-Kwauri Mai Kula da Shiyyar ta Kano/Jigawa, Dalhatu Abubakar, ya ce kayan wadanda suka kai katan 35, an kunshe su ne a cikin buhunan jumbo guda biyar tare da sako su a cikin wata mota kirar Jeep ta alfarma (mai bakin gilaahi).

Hakazalika jami’an hukumar sun cafke wani matashi wanda ake zargi da shigo da kayan, wanda hakan ya saba wa Dokar Hukumar Hana Fasa-Kwauri ta Ƙasa ta shekerar 2023, a cewar Dalhatu Abubakar.

Kwaturola Dalhatu Abubakar ya ce a yayin kamen da suka gudanar da misalin karfe 3:00 na dare a kusa da garin Jalli dake kan Titin zuwa Daura, wanda ake zargi yayi kokarin baiwa jami’ansu cin hancin Naira 455,500.

Kwaturolan shiyyar hukumar ta Customs ya nuna takaici bisa yadda wasu mutane ke shigo da Kwayoyi dake jirkita tunanin jama’a, musamman matasa wanda hakan ke haifar da illa ga lahiya da tunani da jawo aikata muggan lafuka har ma da gurgunta tattalin al’umma.

Daga na, ya yi kira ga kafafen yada labarai su ci gaba da wayar da kan al’umma game da muhimmancin tallafawa jami’an tsaro da bayanan sirri a kokarin dakile aikata muggan laifuka a fadin ƙasar nan.

Da yake karbar kayan da kuma wanda ake zargi daga hannu hukumar Hana Fasa-Kwaurin ta Ƙasa, Daraktan Yaki da Miyagun Kwayoyi na Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), a jihar Kano, Muhammad Usman Mai Adua, ya ce za su zurfafa bincike kafin gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu.

Ya yaba da hadin kai da ake samu tsakanin Hukumar NDLEA da ta Customs, yana mai jinjina wa jagorancin hukumar ta Customs.

A nasa bangaren, wanda ake zargin mai suna Sa’adu Wali, dan unguwar Bachirawa dake cikin birnin Ƙano, ya ce wanda ya doro masa dakon kayan dan Nijar ne kuma ya fada masa cewa kayan karfin maza ne.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *