Tsofaffin Ma’aikatan Tashoshin Tarayya Sun Shirya Gudanar da zanga-zanga Tsirara A Gobe Litinin 8,

IMG 20251207 WA0175

Shugaban ƙungiyar, Mista Mukaila Ogunbote, ya ce za su shiga zanga-zangar ne domin maƙalewar wasu haƙƙoƙinsu da gwamnati ta gaza biya kamar yadda sakataren kuɗi na ƙungiyar tsofaffin ma’aikatan, Bola Popoola ya bayyana cikin wata sanarwa da ya fitar a Legas.

Tsofaffin Ma’aikatan sun bayyana shirin gudanar da zanga-zangar tsirara domin tilastawa gwamnati biyan haƙƙoƙinsu da aka jinkirta biyansu.

Cikin wata sanarwa da shugabannin kungiyar suka fitar, sun bayyana cewa rashin biyan su haƙƙoƙin su da suka haɗa da tallafin rage raɗaɗi na naira 25,000 da jinkirta aiwatar da ƙarin mafi ƙarancin fansho na naira 32,000 ne ya sanya su ɗaukar matakin.

Shugaban ƙungiyar, Mista Mukaila Ogunbote, ya ce matakin ya zama dole saboda tsoffin ma’aikatan sun jima suna jiran biyan haƙƙoƙin nasu. Haka kuma, sun sadaukar da shekaru masu yawa wajen hidimar ƙasa.

Kungiyar ta gargadi cewa zanga-zangar za ta ci gaba a duk faɗin ƙasar har sai gwamnatin tarayya ta biya su haƙƙoƙin nasu.

Bola Popoola, sakataren kuɗin ƙungiyar, ya ce wasu daga cikin tsoffin ma’aikatan da ke zaune a kasashen ƙetare za su gudanar da tasu zanga-zangar tsirara a gobe Litinin domin nuna goyon baya ga abokan aikinsu na Najeriya.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *