Kuyi Kokarin Saka Kano Da Cigabanta Akan Komai Ba Yaɗa Akasin Haka Ba” – Kwamrade Waiya

IMG 20251211 WA1117

Kwamishina Ma’aikatar yaɗa labarai da Harkokin Cikin Gida, Kwamrade Ibrahim Abdullahi Waiya ya bukacin ƙungiyar ‘yan jaridar dake amfani da kafar sadarwa ta intanet dasu kaucewa hanzarin yaɗa labarin dake cike da kurakurai da son zuciya a lokacin wallafa labari musamman wanda ke da alaƙa da tsaro.

Kwamrade Ibrahim Waiya Ya furta haka a lokacin da yake ganawa da mambobin ƙungiyar (Kano Online Media Chapel), a ofishin da dake Sakatariyar Audu Bako a Babban birnin jihar Kano.

Ya ce ya zama wajibi, ƙwarewa da gaskiya gami da aiki bisa ka’ida ya zama linzami ga ‘yan jaridu na online domin samun ɗorewar zaman lafiya da bunƙasar tattalin arzikin ƙasa.

Kwamishina ya nuna damuwa da yadda wata jarida ta wallafa wani labari cewar Kano itace kan gaba wajen sansanin ‘yen ta’adda, wanda yace kuskure ne da kuma neman samun kasuwa.
” Har yanzu babu wani yanki ko ƙaramar hukuma ko wani gari da yake a hannun yan ta’adda a Jihar Kano”.

Kwamrade Waiya, ya bukaci haɗin Kan masu jaridun online da su taimakawa jihar, ta fanin samar da labari na gaskiya da kuma bin dukkanin matakai da suka kamata kafin yaɗa labarai musamman wanda ke da alaƙa da tsaro. A inda ya ce babu burgewa ko ƙwarewa ga Ɗan jarida ya fitar da labarin da zai haifar da asarar rayuka da dukiyar al’ummar dake zaune a ciki, babu-gaira-babu-dalili.

” Mu yi duba da addini da al’ada da jiha da ƙasa baki ɗaya a yayin gudanar da ko wane irin aiki”. Ina ji Kwamishina Waiya.

Ya yabawa ƙungiyar ta yadda suke bayar da rahotonni yadda abubuwa ke gudana a Kano tare da basu tabbacin samun cikakken haɗin kai da goyon baya gwamnati domin samun ɗorewar zaman lafiya a Kano da ƙasa baki ɗaya.

Da yake jawabi shugaban Ƙungiyar ‘yan jaridu na Online, Kwamrade Abubakar Abdulkadir Dangambo, ya godewa Kwamishina da ya kira wannan muhimmin taro bisa hangen nesa na shirya taron domin tunatar da mambobin ƙungiyar game da gudunmawar da suke badawa musamman a fuskar tsaro.

Ka Daina Siyasartar Da Harakar Tsaro, Barau Jibrin Ya Gargaɗi Gwamna Kano

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *