Shugaban Ƙaramar Hukumar  Rimin Gado Ya Kaddamar Da Ginin Katafariyar Gadar Kafofin Yashi

IMG 20251213 WA0873

A ƙoƙarinsa na inganta hanyoyin zirga-zirga da sauƙaƙa rayuwar al’ummar Karamar Hukumar Rimin Gado, Zababben Shugaban Karamar Hukuma, Hon. Muhammad Sani Salisu Jili, ya kaddamar da aikin gina katafariyar gadar Kogin Karofin Yashi, wadda za ta haɗa Mazabar Karofin Yashi da Tamawa, a yau Asabar, 13 ga Disamba, 2025.

Kaddamar da aikin gadar na daga cikin muhimman tsare-tsaren gwamnatin Karamar Hukumar Rimin Gado na tabbatar da hanyoyin zirga-zirga masu ɗorewa, musamman ganin yadda kogin Karofin Yashi ya daɗe yana hana jama’a wucewa cikin sauƙi a lokutan damina, tare da kawo cikas ga kasuwanci, ilimi da harkokin yau da kullum.

A jawabinsa, Hon. Muhammad Sani Salisu Jili ya bayyana cewa ginin gadar wani bangare ne na jajircewarsa na cika alkawuran da ya dauka ga al’umma, yana mai cewa gadar ta daɗe tana ciwa al’umma tuwo a kwarya,amma a yau an fara kawo ƙarshen wannan matsala.

A nasa jawabin, Sakataren Mulki na Karamar Hukumar Rimin Gado, Alh. Sale Adamu, ya jaddada cewa aikin gadar zai taimaka matuƙa wajen haɗa yankuna, bunƙasa tattalin arziki da ƙarfafa tsaro, tare da yabawa Shugaban Karamar Hukuma bisa hangen nesa da mayar da hankali kan ayyukan da ke shafar rayuwar jama’a kai tsaye.

Al’ummar Karofin Yashi da Tamawa sun nuna matuƙar farin ciki da godiya bisa wannan gagarumin aiki, suna mai bayyana cewa kaddamar da gadar wata babbar nasara ce da za ta rage musu wahalhalu da suka daɗe suna fuskanta.

An kammala taron da addu’o’in neman Allah Ya ba da nasarar kammala aikin cikin inganci da lokaci, tare da sanya albarka ga al’ummar Karamar Hukumar Rimin Gado baki ɗaya.

SA HANNU
Arribbabatu Sani Yakasai
Jami ar yada labarai
Karamar hukumar rimin gado

About advertisement or advice call this Number +2348032077835

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *