Gwamnatin Kano Ta Shiryawa ‘Yan Jaridar Yanar Gizo Horon Kwanaki 2, A Dutse Kan Kalubalen Zamani.

IMG 150123 14126 1768399302451

Alfijir – Gwamnatin Jihar Kano ta sake jaddada ƙudirin ta na inganta aikin jaridar yanar gizo bisa gaskiya, ɗa’a da ƙwarewa, inda ta bayyana kafafen yaɗa labaran a matsayin ginshiƙi wajen tafiyar da dimokuraɗiyya.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Kwamaret Ibrahim Abdullahi Waiya, ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake buɗe taron horaswa na kwanaki biyu ga mambobin kafafen yada labarai na zamani [Kano Online Media Chapel] na Ƙungiyar ‘Yan Jarida ta Najeriya (NUJ), wanda ake gudanarwa a Dutse, Jihar Jigawa.

Kwamishinan yace an shirya horon ne kacokan da goyon bayan Gwamnatin Jihar Kano, don basu horo na musamman la’akari da tasirin su cikin jama’a

Taken taron “Ƙarfafa Aikin Jaridar Intanet Ta Hanyar Aiki Bisa Ɗa’a Da Hulɗar Yanar Gizo Mai Dorewa Don Cigaban Jama’a.”

Waiya ya ce wannan horo, shi ne irinsa na farko ga masu wallafa jaridun intanet a Jihar Kano, ya nuna yadda gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ke kallon aikin jarida a matsayin muhimmin ɓangare na tafiyar da ayyukan dimokuraɗiyya.

Kwamishina Waiya ya yaba wa Gwamna Abba Kabir Yusuf bisa amincewa da ɗaukar nauyin bada horon, yana mai cewa hakan alama ce ta jajircewar gwamnati wajen bunƙasa ƙwarewar ma’aikata a fannoni daban-daban, ciki har da kafafen yaɗa labarai.

Kwamishinan ya yi kira ga ‘yan jaridar masu wallafa labarai ta yanar gizo intanet da su riƙa bin ƙa’idojin ɗabi’a, ƙwarewa da gaskiya wajen tattarawa da yaɗa labarai, yana jaddada cewa dole ne a bambanta aikin jaridar intanet da ayyukan kafafen sada zumunta marasa tsari.

Ya ce: “’Yan jaridar yanar gizon ba ɗaya suke da masu amfani da kafafen sada zumunta ba. Aikin jarida na zamani dole ne ya kasance bisa doka da oda, ba wai tayar da hankali ko gaggawar fitar da labari ba tare da tantancewa ba.”

Waiya ya ƙara da cewa saurin bunƙasar dandalin intanet, tare da fitowar sabbin fasahohi kamar basirar (AI), ya sanya wajibi ‘yan jarida su ci gaba da sabunta ilimi da ƙwarewa domin su saje da bukatun ƙasa da ƙasa.

Ya kuma bayyana cewa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida tana fafutukar kafa dokar ‘Yancin Samun Bayanai (Freedom of Information) a matakin jiha, daidai da dokar tarayya, domin ƙarfafa gaskiya, buɗaɗɗen shugabanci da ‘yancin ‘yan jarida a Kano.

Tunda Farko A nasa jawabin, Mukaddashin Babban Sakatare na Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Malam Usman Bello, ya ce gwamnati ta amince da gudanar da taron ne a wajen jihar Kano sakamakon muhimmancin da aikin jaridar intanet ke ƙara samu.

Ya bayyana cewa a baya an taɓa shirya irin wannan taro ga mambobin  Correspondents’ Chapel, yana mai cewa wannan horo an shirya shi ne domin bai wa ‘yan jaridar intanet dabarun da za su dace da sabbin sauye-sauye a aikin jarida bisa ka’idojin zamani na duniya.

Dayake jawabi Shugaban Kungiyar Mawallafin Jaridar Intanet Kwamaret Abubakar Dangambo ya godewa Gwamnatin Jihar Kano da Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida bisa goyon bayan da suka bayar, inda ya bayyana taron a matsayin wani ginshiki wanda yazo daidai da zamani.

Ya yi kira ga mambobin kungiyar da su ci gaba da aiki bisa ƙa’idojin aikin jarida, tare da bin dokoki da tanade-tanaden zamantakewa da na shari’a na Jihar Kano.

Taron ya samu halartar ‘yan jaridu daga kafafen yaɗa labarai na intanet daban-daban da ke aiki a faɗin Jihar Kano.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *