Best Medix 24 ya samo hanyoyin sarrafa magunguna da suka zo a nau’ika na manya zuwa sarrafa su i zuwa na yara ƙanana da zasu iya amfani da su.
Shahararren kamfanin sai da magunguna da harhaɗashi wato Best Medix 24 Pharmacy & Stores ya gudanar da bikin cikar shekaru 4, da fara aiki a ranar 1 ga watan Janairu 2026, in da aka gudanar da taron a jiya Asabar 31 ga watan Janairu 2026 a filin wasanni na Sky Park & Garden dake kan titin jing Road dake Naibawa.
A yayin gabatar da taron ne hukumar gudanarwar ta kamfanin suka karrama ma’aikatan su da suke tsayawa kai da fata wajen kula da abokan kasuwancin su babu dare babu rana, wasu daga cikin ma’aikatan an basu Naira miliyan 1, da lambar girmamawa wasu kuma dubu 60, 70, 80, 100 da lambar girmamawa.
Pharm Ibrahim Muhd Mujittafa wanda shine General Manager na kamfanin Best Medix 24 Pharmacy & Stores, ya bayyana cewa sun shirya wannan taron ne don nuna godiya ga Allah na basu wannan damar na gudanar da wannan kamfanin har zuwa wannan lokacin, da kuma karawa ma’aikatan su kwarin gwiwa na irin ayyukan da suke yi a wannan kamfani, jajircewarsu ta sa muka yi wannan taron domin nuna musu jin dadin mu a gare su.
Shima a nasa bangaren Pharm Abdulmalik Muhd wanda shine Human Resources Manager na kamfanin Best Medix 24 Pharmacy & Stores ya bayyana cewar kamfanin ya samu nasarori da dama a wannan shekarun, amma babbar nasarar da zasu bugi girji da ita itace, yadda al’umma suke samun duk irin nau’ukan abin da suke bukata a koda yaushe kuma a kuma ko ina suke a jihar Kano da wajenta tsawon awanni 24.
Hakazalika kamfanin ya bawa matasa damar samun guraben aiki domin dogaro da kai, sannan kokarin tafiya da zamani duba da yadda abubuwa ke sauyawa a kowane lokuta, wannan ma ba karamar nasara bace, musamman yadda muke kula da abin da ya shafi yanar Gizo domin biya wa customa bukatar sa a kowane lokaci.
A ɓangare guda kuma kamfanin Best Medix ya samo hanyoyin sarrafa magunguna da suke zuwa a nau’ika na manya zuwa sarrafa su i zuwa wanda yara ƙanana da waɗanda aka haifa zasu iya amfani da shi bisa kwarewa da amincewar hukukomi.
Pharm Abdulmalik ya kuma bayyana ire-iren kalubalen da suke samu musamman mu da muke aiki awanni 24, dole muke nemo ma’aikata na musamman domin taya mu kwana saboda bata gari, sannan kuma wani zaka ga yazo babu takardar likita yace sai an bashi magani, wanda a tsarin mu, bama bada magani sai da takardar likita ko kuma wasu ƴan tsirari da aka yadda a bayar, idan muka hana sai kaga wani lokacin har da zagi! Amma ba yadda muka iya dole mu yi hakuri, kuma dai babu wata nasara da take tabbata ba tare da ƙalubale ba, don haka sai dai muce alhamdulillah.
Best Medix 24 Pharmacy & Stores ya fara ne da wajen daya, amma yanzu haka muna da reshe guda 3, na farko yana nan a tal’udu kusa da gidan Alaramma kafin a tsallaka titi, sai kuma na shima akan titin tal’udu kusa da makarantar Sheikh Bashir El Rayyan bakin asibitin Best Choice, Sai Kuma aikin na 3 da muke wanda idan an kammala za’a sanar da al’umma.
A ƙarshen Pharm Ibrahim yayi kira da al’umma da su mai da hankalin su wajen neman ingantaccen magani fiye da bin sauki, domin ita lafiya ba’a yi mata danganci, Best Medix 24 mun yi fice wajen lalubo muku ingantattun magunguna a duk inda suke domin biyan bukatunku.



Taron ya sami halartar manyan manyan jami’an lafiya da wasu daga cikin manyan dilolin magunguna na jihar Kano kamar:
1. Pharmaceutical Society Of Nigeria, Kano Chairman
Pharm Murtala Isa Umar
2. Pharmacy Council Of Nigeria, Kano Coordinator
Pharm Hasiya Ladan
3. Association Of Community pharmacists Of Nigeria, Kano Chairman
Pharm Muhammad Tukur Sulaiman
4. Wakilin Shugaban kamfanin Latnas Pharmacists
Muhammad Shitu Madigawa
5. MD MGK Pharmacy. Alh Muhammad
6. MD Grand Medicos. Pharm Idris Musa Bagwai
7. MD Al- Fatah Pharmacy. Pharmacy Musbahu
8. MD Eagles Mad Pharmacy. Pharm Sulaiman
Sai waɗanda suka taimaka wajen gudanar da taron
Young Focus Ventures
Alh Nafiu Ibrahim
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t