Nasarori da Iran ta samu bayan kai munanan hare-hare Tel Aviv da Jerusalem da Yammacin Kogin Jordan yau Juma’a

FB IMG 1772798201114

Bayan munanan hare-haren da Iran ta kai tsakar birnin Tel Aviv na Isra’ila a safiyar yau Juma’a da bayanai ke cewa ya kashe mutane masu yawa tare da rushe tarin gine-gine irinsa na farko da ya tsananta, wanda kuma ya shafi ƙarin biranen ƙasar ta Yahudu ciki har da Yammacin gaɓar Kogin Jordan da Jerusalem, masharhanta sun fara tsokaci kan yadda ƙasar ke ci gaba da iya mayar da martani duk da luguden wutar haɗin gwiwar da ake ci gaba da yi mata tsakanin Amurka da Isra’ila.

Bayanai sun ce tuni Isra’ilar ta mayar da martani wajen kai sabbin hare-hare zuwa tsakar birnin Tehran da sauran biranen Iran ciki har Qom wanda ya shafi cibiyar horas da sojoji, a wani yanayi da Amurka ke iƙirarin cewa makamai sun fara ƙarewa ƙasar ta yankin Gabas ta Tsakiya.

Tuni dai Iran ta aike da saƙon jan kunne ga Isra’ilan kan cewa ta jira ƙarin munanan hare-hare kowanne lokaci daga yanzu a wani yanayi da ma’aikatar tsaron Amurka ke iƙirarin cewa Tehran ta fara shure-shure kuma nan gaba kaɗan manufarsu za ta cika a ƙasar.

A cewar ma’aikatar tsaron Amurkan yanayin yawan makaman da Iran ke harbawa cikin kwanaki 6 da yini 7 da faro wannan yaƙi da kuma hare-harenta a yau Juma’a ya nuna cewa ƙarfinta ya fara ƙarewa kuma ba ta da wadatattun makaman iya kai hare-hare a yanzu.

Sai dai Iran na ci gaba da cewa a yanzu ne za ta tsananta hare-hare tare da farmakar duk wasu manufofi ko kadarorin Isra’ila a duk inda suke a ba kaɗai a yankin ba.

A gefe guda jagoran dakarun juyin juya hali na Iran Ali Larjani ya buƙaci Amurka da ta gaggauta aiko da sojojinta na ƙasa domin dakarunsu na zaman jiran isowarsu.

Wannan na zuwa a dai dai lokacin da aka fara ganin hare-haren tsirarin ƙungiyoyin da ke marawa Iran baya kan manufofin Amurka bayan da ƙungiyar Saraya Awliya al-Dam mai riƙe da makamai a Iraqi ta ɗauki alhakin harin Jordan.

Yanayin tirjiyar Iran wajen mayar da martani a hare-haren da ake ci gaba da kai mata ya bayar da mamaki matuƙa koda yake masana yankin irin Ambassada Abubakar Cika, tsohon Jakadan Najeriya a Iran ke cewa ƙasar ta huce yadda ake tunaninta, haka zalika wannan yaƙi zai tunzurata wajen mallakar makamin nukiliya.

RFI Hausa

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *