Garkame Mashigin Tekun Hormuz, Jiragen Ruwa 3,000 da dubban Ma’aikatan Teku Sunata Gararanba a Gabas ta Tsakiya – Inji IMO

IMG 20260307 WA0409

Daga Aminu Bala Madobi

Kungiyar kulada tekuna ta kasa da kasa International Maritime Organization (IMO) ta bayyana cewa akalla jiragen ruwa 3,000 da ma’aikatan teku 20,000 ne suka makale a yankin Gabas ta Tsakiya sakamakon yaƙin da Amurka da Israel ke yi da Iran.

Muhimmin mashigin ruwa na duniya mai suna Strait of Hormuz, mallakin Iran ya zama wata hanyar shiga Tekun Fasha (Persian Gulf), Kasar Iran ta garkame sa gaba ɗaya saboda barazanar hare-hare da sauran haɗurra a yankin, a cewar IMO.

Sakatare Janar na IMO, Arsenio Dominguez, ya yi gargaɗin cewa rufe wannan hanya zai haifar da mummunar illa ga tattalin arzikin duniya, domin kusan kashi 20 cikin 100 na man fetur na duniya na bi ta wannan mashigin ruwa.

Dominguez ya ce an rufe mashigin ne bayan wani ƙaramin jirgin taimako (tugboat) da ke taimaka wa wani jirgi a mashigin a safiyar Juma’a ya gamu da mummunan hari, wanda ya yi sanadin mutuwar ma’aikatan teku huɗu.

Shugaban hukumar jigilar ruwa ta Majalisar Ɗinkin Duniya ya yi Allah-wadai da harin, yana mai cewa halin da ake ciki a yankin na ƙara taɓarɓarewa, sannan ya buƙaci jiragen ruwa su guji zirga-zirga a yankin.

Ya kuma roƙi ƙasashe mambobi su nemi mafita ta hanyar tattaunawa domin rage tashin hankali da kuma dawo da zirga-zirgar jiragen ruwa cikin aminci.

Jami’in kula da agajin gaggawa na Majalisar Ɗinkin Duniya, Tom Fletcher, ya yi gargaɗin cewa faɗaɗar rikicin Gabas ta Tsakiya na iya jawo matsalolin jin kai da za su wuce yankin.

Fletcher ya ce katsewar manyan hanyoyin ruwa kamar Strait of Hormuz na iya janyo tashin farashin abinci a duniya. Ya ƙara da cewa hakan na iya matsa lamba ga tsarin kiwon lafiya tare da wahalar da kai agajin jin kai ga mabukata, inda mafi rauni a cikin al’umma za su fara fuskantar illa.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *