Cikin girmamawa nake maka sallama Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu ya ibada Allah ya karba mana ameen ameen.
Mai girma Gwamna zan iya tunawa da bayaninka bayan komawarka jam’iyyar APC, kayi wani bayani mai ratsa jiki! Inda kake cewar kai Allah zai tsayar ya tambaye ka yadda kayi da dukiyar al’ummar kano bayan da suka zabe ka ka zama gwamna!
Mai girma Gwamna wannan bayanan naka ne suka zaburar dani, kan ya zama dole nayi iyakar iyawa ta wajen taimaka maka wajen cikar wannan buri naka da amanar da al’ummar Kano suna dora maka.
Abba ka cika Gwarzo
Nima dai nace bara na dana wannan kirarin da masoya ke maka, domin da ba don kana son kyautatawa al’ummar Kano ba da yanzu ba wannan zancen ake ba a jihar, da tuni ana waje daya ana dabon kwalo.
Mai girma Gwamna kai tsaye abin da yasa nake wadancan zantuka, ina yin su ne domin in yaba maka yadda kayi nazari wajen sallamar shugaban ma’aikatan jihar, domin a sake kawo sauyi! Sai dai kuma mai girma gwamna ba iyaka cin shugaban ma’aikata ya kamata ka waiwaya ba kawai har da sauran wadanda ka nada don taimaka maka.
Rijiya ta bada ruwa guga fa yana hanawa!
Ka nemo mutane da dama wadannan ka nada su mukamai daban-daban domin su taimaka maka wajen sauke nauyin da al’umma suka dora maka, amma wallahi wallahi duk da bana rantsuwa mai girma gwamnan abin ba haka yake ba!
Kafin wannan rubutun domin gudun zargi, sai da muka yi zagayen kuturunka nawa a kusan ma’aikatun jihar domin ganin irin yadda suke gudanar da ayyukan da ka basu, sai dai abin takaici lamarin ya kazanta, domin da yawa daga cikin wadanda kai ma ka bawa wannan amanar sun sauka daga layin, suna yin abinda suka ga dama, idan aka nuna musu sun sauka daga layin yadda ake tafiyar da aikin, sai wasunsu suce ai kawo su kayi su ci wani abu ba su sha wahala ba!
Wannan dalilin yasa na tuna da wancan iƙirarin da kayi na cewar kai Allah zai tsayar ya tambayeka yaya kayi da dukiyar al’ummar jihar Kano, hakan tasa nake rubuta maka wannan Wasika tunda bani da yadda zan yi na ganka, amma nasan akwai masoyanka masu burin ka gama lafiya da muke tare dasu da nasan insha Allah zasu tura maka wannan sakon.
Allah ya taimaki Kano da mutanen Kano
Allah ya karawa kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali ameen summa ameen.
Naka mai kaunar ka gama lafiya da wannan nauyin da al’umma suka dora maka.
Malam Muhammad Na Muhammad
Masoyin Abba Gida Gida
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t