Labari Mai Dadi: hukumar DSS ta kuɓutar da sakataren mulki na Karamar hukumar Kibiya a Kano

IMG 174503 25326 1774457116342

Hukumar tsaron farin kaya ta DSS ta sanar da kubutar da Sakataren Mulki na Karamar Hukumar Kibiya da ke Jihar Kano, Hon. Hamza Musa Durba, bayan da aka yi garkuwa da shi.

A cewar rahotanni, jami’an tsaron sun gudanar da wani samame a wani daji da ke yankin Kibiya, inda suka samu nasarar ceto jami’in gwamnati ba tare da ya samu wata illa ko biyan kuɗin fansa ba.

Majiyoyi sun bayyana cewa jami’an sun fara tattaunawa da wadanda suka yi garkuwa da shi ta wayar tarho, lamarin da ya taimaka musu wajen gano maboyar wadanda ake zargin.

Rahoton ya kara da cewa jami’an DSS sun kama mutane biyu daga cikin wadanda ake zargi, inda aka same su da bindiga kirar AK-47. Shi kuma Hon Hamza hukumar DSS ta tura shi domin duba lafiyarsa sannan a dankawa iyalansa.

A halin yanzu, hukumomin tsaro sun ce ana ci gaba da bincike domin gano sauran wadanda ke da hannu a lamarin

Hukumar DSS hukuma ce da take kokarin kare rayuwa da dukiyar al’ummar kasa da jihar Kano baki daya muna addu’ar Allah ya taimaki wannan hukumar ya kuma kare su daga dukkan sharri ameen ameen.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *