Sarkin Guragun kano Lawan Ibrahim ya koka akan yanda aka basu wa’adin watanni 3 su tashi daga Inda suke zaman Fadar Masarautar Guragun kano.
Masu bukata ta musamman Karkashin jagorancin Sarkin dake zaune a kan titin katsina daura da Shatale talen Baban Gwari ta Bakin Sarkin sunce basu da inda zasu koma kuma basu da kudin da zasu kama hayar wani wajen.
A yayin ziyarar gani da Ido, wakilin mu ya tarar da masu bukata ta musamman din, kowa yana gudanar da aikin sa na sana’oin hannu musamman yanda ake hada Keken Guragu, Sandar Dogarawa, Baburin Guragu dadai sauran su.
A don haka ne suka mika koke ga Mahukunta musamman gwamnatin kano ta kawo musu dauki ta samar musu da wani wajen da za su Cigaba da Neman Abincin su, Wanda a cewar Sarkin Sama da mutane Masu bukata ta musamman Sama da 200 ne ke Cin Abinci a wajen tsawon shekaru 20 da suka gabata.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t