EFCC ta kama tsohon ministan wutar lantarki, Saleh Mamman

FB IMG 1779207387882

Hukumar yaƙi da masu yi wa Tattalin arzikin ƙasa ta’annati ta EFCC ta kama tsohon Ministan wutar lantarki, Saleh Mamman, bayan ya shafe lokaci yana ɓuya duk da hukuncin ɗaurin shekaru 75 da aka yanke masa.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an EFCC sun cafke Mamman ne a unguwar Rigasa da ke jihar Kaduna da misalin ƙarfe 3:30 na daren  Talata.

Shugaban hukumar EFCC, Ola Olukoyede ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ke gudana a hedikwatar hukumar.

A cewar Olukoyede, an samu nasarar kamo tsohon ministan ne bayan bincike da bibiyar da jami’an hukumar suka yi.

Ana sa ran hukumar za ta fitar da ƙarin bayanai kan yadda aka kama shi da kuma matakan da za a ɗauka a kansa.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *