A Karon Farko Tinubu Ya Amince Da Ƴan Najeriya Na Fama Da Talauci A Faɗin Ƙasar

FB IMG 1771423167430

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yadda cewa ‘yan kasar na fama da matsalolin tattalin arziki abin da ya jefa su cikin mawuyacin hali.

Tinubu ya bayyana hakan yayin da yake karbar takardar tabbatar da cin zaben cikin gida na jam’iyyar APC a kakar zaben 2027 a ranar lahadi.

Da yake tabbatar da matalolin da ake fuskatan a fannin tattalin arziki a kasar, Tinubu yace “duk da cewa akwai kalubale a gabanmu. ‘yan Najeriya da dama na ci gaba da fuskantar matsi ta hanyar tashin farashi da kalubalen tattalin arziki.

“Mun dauki wannan da mahimmanci; muna duba hanyar da zamu samar da sauki, amma ta hanyar da muka fahimta, da gaskiya tare da daukar matakai na bai daya.”

Haka kuma, Shugaban Kasa ya amince cewa matsalar tsaro ta na kara Kamari a wasu sassan kasar nan, duk da kokarin da dakarun soji ke gudanarwa.
Tinubu ya ce: “Na san cewa har yanzu akwai kalubalen tsaro dake fuskantar wasu sassan kasarmu mai girma.”

Ya kara da cewa gwamnatinsa ta zuba kudade masu yawa a bangaren tattara bayanan sirri, sanya idanu, da kuma amfani da na’urorin tsaro na zamani.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *