Gwamnatin Kano Ta Bada Umarnin Daukar Fasinjoji Kyauta A Motocin Kanawa

Alfijr ta rawaito Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya amince da Motocin Kanawa Bus Service da su fito su fara jigila kyauta domin kai al’ummar jihar Kano wuraren sana’oinsu, ofisoshinsu da Makarantu don saukaka musu a bisa wannan rashin wadatattun kudi da aka shiga a fadin kasar nan.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da tsohon sakataren gwamnatin Kano, kuma daraktan yaÆ™in neman zaÉ“en jam’iyyar APC na jihar Kano a zaÉ“en shekarar 2023, Injiniya Rabiu Sulaiman Bichi, ya fitar

Bichi yace za’a fara Jigilar ne a gobe Litinin, don haka ake umartar jama’a dasu zama masu da’a da biyayya wajen hawa wannan Motoci.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *