Kotu Ta Umarci Gwamna Ganduje Da Ya Dawo Da Muhuyi Mukaminsa

Alfijr ta rawaito Kotun Masana’antu ta Ƙasa da ke zamanta a Kano, a yau Litinin ta umurci gwamnatin jihar Kano da ta yi biyayya ga halin da ake ciki a da, na ayyana Muhuyi Magaji Rimingado da ta kora a matsayin shugaban hukumar yaki da cin-hanci da rashawa ta jihar, a ƙarar da ya shigar har sai ta saurari korafe-korafensa.  

An shigar da karar a gaban mai shari’a E.D. Esele, in da gwamnatin jihar Kano da majalisar dokokin jihar da kuma babban lauyan jihar Kano a matsayin wadanda ake tuhuma na 1 da na 2 da na 3.

Muhuyi shigar da karar ne yana kalubalantar sahihancin matakin da gwamnati ta dauka na korar shi ba tare da bin ka’ida ba.

A bisa wannan umarnin, wasikar korar da aka mika wa Rimingado ba ta da wani tasiri, inda kuma hukuncin da kotun masana’antu ta kasa a Abuja ta yanke a baya ya na nan sai dai idan kotu ta yanke hukunci saɓanin wannan na baya.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/F86a4baiSZU4aMOt7yuBfE

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *