Da Ɗumi Ɗuminsa! Magoya bayan APC na gudanar da zanga-zanga a Kano

Alfijr ta rawaito Daruruwan magoya bayan jam’iyyar APC ke gudanar da zanga-zangar lumana a ofishin hukumar zabe ta INEC da ke a jihar Kano.

Masu zanga-zangar na bukatar hukumar zaɓe ta sake nazari kan sakamakon zaben gwamnan jihar.

Hukumar zaɓen dai ta bayyana Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar adawa ta NNPP a matsayin wanda ya yi nasara a zaɓen.

Bayan doke babban abokin hamayyarsa Nasiru Yusf Gawuna na jam’iyyar APC mai mulkin

Masu zanga-zangar sun ce kamata yayi a ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba

Jam’iyyar ta APC dai ta kuma miƙa wa hukumar INEC takardar ƙorafinta game da zaɓen

BBC

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Alfijr Labarai
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ

2 Replies to “Da Ɗumi Ɗuminsa! Magoya bayan APC na gudanar da zanga-zanga a Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *