Alfijr ta rawaito tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriyya sanata Ike Ekweremadu da ake zargi da yukurin cire kodar wani mutum don a saka wa yarsa da ke fama da rashin lafiya / Hoto: AFP
Wata kotun Birtaniya ta yanke wa tsohon mataimakin shugaban majalisar dattawan Nijeriya Ike Ikweremadu daurin kusan shekara goma a kurkuku.
Kotun ta yanke hukuncin ne bayan samun tsohon dan majalisar dattawan da mai dakinsa da wani mutum da laifin yunkurin cire kodar wani matashi domin sanyawa ‘yarsa da ke fama da ciwon koda.
Kotun ta Old Bailey da ke Landan ta yanke wa mai dakinsa Beatrice hukuncin zaman gidan yari na shekara hudu da wata shida.
A watan Maris ne kotun ta samu Mista Ekweremadu, Sanata a Majalisar dattijan Nijeriya da matarsa Beatrice, da laifin hada baki wajen safarar matashin mai kimanin shekara 21, da ke sana’ar sayar da kaya a kan tituna a Jihar Legas zuwa Burtaniya don a cire masa wani sashe na jikinsa a dasa wa ‘yarsu, Sonia.
Wannan dai shi ne karon farko da aka taba gabatar da tuhume-tuhume kan hada baki don a cire wani sashe na jikin dan adam a karkashin dokar bautar zamani ta 2015 a Burtaniya.

Ike Ekweremadu, wanda alkalin ya bayyana “a matsyain musabbain faruwar komai,” an yanke masa hukuncin daurin shekara tara da wata takwas.
Yayin da ita kuma matarsa Beatrice Ekweremadu aka yanke mata hukuncin daurin shekara hudu da wata shida saboda rashin samunta da hannu dumu-dumu a lamarin ba.
Sannan shi kuma likitan Dr Obeta aka yanke masa hukunci daurin shekara 10 bayan da alkali ya gano cewa ya so ya cire kodar matashin wanda ba shi da gata.
Dokar dai ta yi hani kan fataucin dan adam inda cire duk wani sashe na jikin mutum ya fada ciki, kuma hukuncin duk wanda aka kama da laifin hakan shi ne daurin rai-da-rai
A shari’ar da aka kwashe tsawon watanni ana yi, matashin wanda ba a bayyana sunansa ba saboda dalilai na shari’a, ya bayyana cewa Ekweremadu ya kai shi Biritaniya don a cire masa kodarsa.
An yi kokarin dasa kodar ne wa Sonia wacce ake yi wa aikin wanke koda da har ya kusan daina aiki, kan kudin Fam 7,000 kwatankwacin dala 8,800
Matashin ya bayyana cewa likitan da ke yiwa dan siyasar aiki da ne ya dauke shi aiki, kuma a tunaninsa zai kai shi Birtaniya ne don ya samu aikin yi.
Sai daga baya ya gane cewa an kai shi Kasar ne don a cire masa kodarsa lokacin da ya ga kanshi a asibitin Royal free dake Landan a shekarar da ta gabata, kamar yadda aka shaida wa kotu.
Ya gudu ya kwana a titi na tsawon kwanaki uku, bayan da likitocin da ke asibitin sun shaida masa cewa ba zai ba da gudummowar da ya dace wanda ake nema ba bayan gwaje-gwajen farko.
Daga karshe ya shiga ofishin ‘yan sanda a watan Mayun shekarar bara ya na mai neman “wanda zai ceci rayuwata”, kamar yadda kotun ta ji.
Lauyoyin mutane hudun da ake tuhuma sun dage kan cewa matashin ya na “wasan kwaikwayo ne”, ana shi bangaren Sanata Ike Ekweremadu ya shaida wa alkalan kotun cewa yana jin tsoron “a damfare shi”.
Ekweremadu ya wakilci mazabar Enugu ta yamma a kudu maso gabashin Najeriya a jam’iyyar adawa ta Peoples Democratic Party tun daga shekarar 2003.
Majalisar dokokin Najeriya a wannan makon ta roki hukumomin Burtaniya da su yi sassauci ko yafewa Sanata Ike Ekweremadu kan laifin da a ka same shi na neman yanke kodar wani matashi don dasawa ‘yar su da ke bukata.
Majalisar ta ce Ekweremadu ya bayar da gudunmowa mai tsoka a harkokin siyasa a yammacin Afirka kuma wannan shi ne karon farko da aka taba sanub sa da laifi irin wannan.
ko da ya ke bai samu damar tsayawa takara ba a zabukan ‘yan majalisar dokokin kasar na baya-bayan nan saboda yana tsare saboda tuhumar sa da ake yi.
Laifukan da ake zargin su da aikatawa sun faru ne tsakanin watan Agustan shekarar 2021 zuwa Mayun 2022
TRT Afrika
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/G1wNveF9mGU7jec5mWhFvZ