Shugabar Kotun Daukaka Kara, Mai Shari’a Monica Dongban Mensen, ta ce kotun daukaka kara na da shari’o’i 39,526.
Alfijir Labarai ta rawaito mai shari’a Mensen ta bayyana haka a yayin bikin kaddamar da sabuwar kalanda shekarar shari’a ta 2023/2024.
Ta ce kotun daukaka kara ta samu jimillar kararraki dubu 7,295 da kuma kararraki 3,665 a shekarar 2022/2023.
“A shekarar shari’a ta 2022/2023, an shigar da jimillar kararraki 7,295 da kuma ƙorafe-ƙorafe dubu 3,665 a sassa 20 na kotun.
” Kotu ta kammala kararraki dubu 3,765 sannan ta kori kararraki 5,617.
An kori 1,030 daga cikin waɗannan kararraki kuma an ba da izini a kan 10,381.
“Har yanzu kotun tana da jimillar kararraki 39,526 da ake sauraro zuwa ranar 31 ga watan Agusta, 2023.
Wannan karuwa ce daga dubu 34,037 da ke gaban kotu a shekarar shari’a ta 2021/2022,” in ji ta.
Ta ce an samar da kwamitocin shari’a 98 domin sauraren ƙorafe-ƙorafen zabe a fadin kasar nan domin gudanar da jimillar korafe-korafe 1,209 da aka shigar.
Daily Nigerian
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb