Alƙalin Babbar Kotun Shari’ar Muslunci da ke Ƙofar Kudu Ustaz Ibrahim Sarki Yola ya nemi Gwamnati ta riƙa bai wa alƙalan Kotunan Musulunci kulawa, musamman waɗanda su ke ƙauyuka.
Alfijir labarai ta rawaito Sarki Yola ya ce, abin takaici ne za a samu alƙali ya gama shari’a a Kotu, sannan a ganshi a layin hawa Mota a tasha, har ma wani lokaci su yi kafada da kafada da wanda ya yiwa shari’a a Kotun.
Mai shari’ar ya bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da littafin da Alƙali Abdu Abdullahi Wayya ya wallafa mai suna “Iƙrari, Shaida da Rantsuwa”.
Alkali Yola dai shine a baya ya yanke wa wani Malamin Ɗariƙar Ƙhadiriyya a Jihar Kano Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara hukuncin Kisa, inda al’ummar Kano da dama suka jinjina masa saboda yadda ya jajirce wajen hukunta Abduljabbar din, bayan da ya taba muhibbar shugaba S A W.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk