Al ummar Arewacin Nigeria Sun Shirya Wa Buhari Gagarumar Zanga-Zanga

 

Al ummar Arewacin Nigeria Sun Shirya Wa Buhari Gagarumar Zanga-Zanga

Best Seller Channel 

Best Seller Channel 

Al ummar arewacin Najeriya sun shirya gagarumar zanga-zanga kan rashin tsaro da kisan gillar da ’yan bindiga ke yi babu kakkauta wa yankin.

Jaridar Aminiya ta rawaito Cewar zanga-zangar ta zo ne bayan Buhari ya halarci taron kaddamar da littafin tarihin wani jigo a jam’iyyar APC a Jihar Legas, Cif Bisi Akande, inda a daidai lokacin da ’yan bindiga suka tare matafiya masu yawa suka kona su kurmu a Jihar Sakkwato, amma bai je can ba.

Best Seller Channel 

Aminiya ta ce, a safiyar Juma’a ce aka fara zanga-zangar a Abuja da sauran wurare, a yayin da ’yan Najeriya ke ta sukar Shugaba Buhari kan nuna halin ko-in-kula da kisan gillar da ake yi a yankin Arewacin kasar.

Jama a na ta surutai kan halartar taron kaddamar da littafin tarihin Bisi Akande a Legas a ranar Alhamis da shugaba Buhari yayi, alhali yana sane da kisan gillar da ’yan bindiga suka yi wa matafiyan a Sabon Birni ta Jihar Sakkwato.

Best Seller Channel 

Da yawa daga cikin masu sukar shi, sun nemi ya sauka daga mukaminsa, saboda a cewarsu, bai kare rantsuwar da ya yi na kare rayuka da dukiyoyinsu yan kasar ba, sannan ya nuna bai san nauyin da ya rataya a wuyansa ba.

Ranar Alhamis ne, shugabannin Sabon Birni suka aike masa da wasikar bacin ransu kan yadda gwamnatinsa ta bar ’yan bindiga suka mayar da rayukan jama’arsu ba a bakin komai ba.

Aminiya ta ce, masu zanga-zangar a Abuja za su yi tattaki ne daga Unity Fountain zuwa Majalisar Dokoki ta Kasa, domin bayyana fushinsu kan rashin katabus din gwamnati wajen magance matsalar tsaro a yankin Arewacin Najeriya.

Tun a ranar Alhamis, kungiyar Jama’atu Nasril Islam, babbar kungiyar Musulunci a Najeriya ta aike wa Buhari wasikar kar-ta-kwana kan matsalar tsaron da ya ki ci, ya ki cinyewa, musamman a yankin Arewa maso Yamma.

Best Seller Channel 

’Yan bindiga a yankin sun kashe dubban mutane ciki har da dalibai da mata da kananan yara da jami’an tsaro; Sun yi wa mata mata fyade.

Slide Up
x