Yan Sanda Sun Rufe Wurin Da Aka Ba Wa Muhuyi Magaji Domin gabatar da Lakcar, ranar yaki da cin hanci da rashawa ta Duniya

 Yan Sanda Sun Rufe Wurin Da Aka Ba Wa Muhuyi Magaji Domin gabatar da Lakcar, ranar yaki da cin hanci da rashawa ta Duniya. 

Best seller Channel 

Best Seller Channel 

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano a ranar Alhamis ta rufe wurin da aka shirya gudanar da bikin ranar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya na shekarar 2021 a birnin Kano. 

 Jaridar Nigerian Tracer ta rawaito Cewar, bikin na shekara-shekara da kungiyar Concerned Citizen ta jihar Kano ta shirya ya ci karo da juna lokacin da jami’an ‘yan sanda suka bayyana a wurin da aka yi hayar don gudanar da taron tare da umurtar mahalarta taron da su watse.

Best Seller Channel 

 Daruruwan matasa ne suka hallara a Leena Events Center dake kan titin Muhammadu Buhari daura da Jami’ar Yusuf Maitama Sule da ke unguwar Kabuga, inda aka bukaci tsohon Shugaban Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa ta Kano, Muhuyi Magaji-Rimingado ya yi jawabi. 

Matasan sun gayyaci tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Magaji, domin ya yi tsokaci kan yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya. 

Best Seller Channel 

Hauwa Adamu, daya daga cikin mahalarta taron ta shaida wa manema labarai a Kano cewa, muna wajen taron, kwatsam sai ga wasu jami’an tsaro suka ce mu watse.

Hauwa Adamu ta bayyana cewa, jami’an tsaro sun shaida wa mahalarta taron da suka ji takaicin abin da suka yi shi ne ya sa aka ba su umarni daga C I D. 

Best Seller Channel 

Ta kara da cewa wasu ma’aikatan hukumar tsaro da farin kaya ta Najeriya sun raka jami’an da suka rufe wurin taron. 

Da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa domin jin ta bakinsa, ya ce bai san da faruwar lamarin ba. 

DSP Kiyawa ya yi alkawarin gudanar da bincike ya dawo, amma har zuwa lokacin da za a hada rahoto, ba a ji komi daga gare shi ba.

Slide Up
x