Shahararren dan kasuwan nan, Alhaji Aminu Dantata ya ce tsarin shugabancin firaminista da wasu ’yan majalisa suke nema shi ne mafi alheri ga kasar nan.
Alfijir labarai ta Dantata ya bayyana haka ne a lokacin da wasu ’yan majalisar wakilai karkashin jagorancin shugaban marasa rinjaye, Kingsley Chinda suka kai masa ziyarar neman shawara a gidansa da ke Kano a ranar Alhamis.
Alh Aminu Dantata ya ce, “Na gode da wannan ziyara, kuma ina yi wa wannan gagarumin gangami addu’ar samun nasara.
“Tsarin firaminista ne ya fi dacewa da kasar nan, saboda babu kashe kudin gudanarwa kaman tsarin shugaban kasa da muke bi.
“Ina fata za ku samu goyon bayan abokan aikinku, kuma ina rokon Allah Ya ba ku basira, ya yi muku jagora wajen cimma wannan kyakkyawan manufa ta taimakon kasar nan.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V