Alh Musa Jidda Ɗan Adalan Mubi Na Taya Daukacin Al’ummar Annabi SAW Murnar Maulidi

IMG 20250626 WA0965

Alh Musa Jidda Ɗan Adalan Mubi Saraki ya ce, ina taya al’ummar musulmin duniya dana Najeriya tare da na wannan jiha tamu mai albarka ta Kano murnar zagayowar watan Maulidi, watan da aka haifi shugaban halitta Annabi Muhammadu Sallallahu alaihi Wasallama

Ina kira ga al’umma Musulmi da su dage da addu’a a wannan watan na Maulidi domin samun ingantacan tsaro da kuma tattalin arziki mai dorewa a fadin kasar nan da jihar Kano mai albarka.

Haka zalika ina kira da mahukunta da su kyautata rayuwar marasa karfi da samawa matasa ayyukan yi domin magance wannan masifar daba da ƙwacen wayar da ake fama da ita, ta wannan hanya ce za a iya inganta rayuwar al’umma.

12 ga watan Rabi’ul Awwal ita ce ranar da aka haifi fiyayyen halitta Annabi Muhammad (SAW). Kuma rana ce da musulmi ke alfahari da ita ta hanyar shirya karatuttuka da sada zumunci da liyafar cin abinci da kasidu domin nuna murna.

Allah ya taimaki jihar mu ta kano da kasar mu baki daya ya inganta rayuwar al’ummar mu, ya kara mana lafiya da zaman lafiya Ameen.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *