Allah mai tsarki ne shi kuma baya karbar komai sai mai tsarki – Tunatarwar Sheikh Ali Dan Abba Ga Yan Kasuwa

IMG 20250221 013116

Hukumar Shari’a ta jihar Kano tare da mambobinta da wasu daga cikin ma’aikatanta sun fara ziyarar gyara kayanka domin neman dacewa da rahamar Allah.

Inda a yau Alhamis aka kai ziyara ta musamman ga hukumar kasuwannin ta jihar jihar Kano karkashin jagorancin Kwamishina na biyu Malam Ali Dan Abba da Kwamishina na É—aya Gwani Hadi tare da babban darakta na hukumar Dr Sani Ashir da Mambobin hukumar da daractoci tare da ma aikata

Bayan bude taro da Gwani Hadi yayi da karatun Alqur’ani sauran malamai irinsu Malam Abubakar Mai Ashafa sunyi jan hankali ga yan kasuwa sai wakilin shugaban hukumar Malam Ali Dan Abba ya fara da cewar:-

Watan Ramadana wata ne na tsoron Allah don haka yan kasuwa kuji tsoron Allah ko a dace da rahamar Allah. Wannan shine babban burin mai girma Gwamnan Kano ya ga an saukakawa al’umma musamman a watan mai albarka na Ramadana da zamu shiga.

Malam Ali Dan Abba ya kara da cewar kamar yadda likitoci, malamai ,da sauran bangarorin rayuwa kafin a yadda da shahadarsu sai an basu horo na musamman sannan ake amincewa da ayyukansu, to ya zama wajibi ma yan kasuwa sune ilimin kasuwanci duba da Musulunci yana da tsari, kuma bai yadda kowa yayi alkafirar daya ga dama ba.

Ya kara da jan hankalin yan kasuwa da masu kuÉ—i kan cewar mu tuna fa cewar duk abin da muka tara sai an yi mana hisabi akansa da kwabo da dari! Don haka ba dai dai bane a shiga kasuwanci ana ta matse jama a da gallaza musu ba

Dan Abba ya kuma ja hankalin yan kasuwa wajen hadarin da yake tattare da al’adar nan da wasunsu suke yi ta boye kayan da zummar a tari wani lokaci don gallazawa al’umma. Da kuma jagwalgwala harkar tsakanin mai kyau da maras kyau! Bayan kuma shi Allah Dayyiban ne, wato mai tsarki ne shi kuma baya karbar komai sai mai tsarki, don haka ya kamata mu kara kwana da sanin wannan.

Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya gaya mana cewa abubuwa 3 zasu raka mutum kabarinsa amma fa 2, zasu dawo! Akwai iyalinka da dukiyar ka duk zasu dawo aikinka ne kawai zai zauna tare da kai.

A karshe yayi addu’a ga yan kasuwarmu musamman masu jin kan al’umma da jihar Kano da fatan Allah yasa ayi Ramadana da mu kuma Allah ya sa mu cikin yantattun bayi.

A karshe shugaban hukumar kasuwanni ta jihar Kano ya yaba da wannan ziyarar ya kuma tabbatar da cewar dama faduwa ce ta zo dai dai da zama, domin dama akan wannan aikin suke kamar yadda mai girma Gwamnan Kano Abba Kabir yake umartarsu a kowane lokaci.

Don Muna maraba da wannan ziyarar a ko da yaushe domin a gudu tare a tsira tare.

A karshe ya ja hankalin yan jarida wajen jajircewa akan aikinsu tare da tabbatar da gaskiya da sanin Yakamata a aikinsu.

For more information about  Alfijir labarai/Alfijir news follow here  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *