Yadda Wasu Manya A Kasa Da Wasu Kasashen Afirka Suka Hallara A Bikin Kaddamar Da Littafin Tarihin Rayuwar Ibrahim Babangida

FB IMG 1740057773982

Tsoffin shugabannin Najeriya da na ƙasashe masu maƙwabtaka da sauran masu faɗa a-ji a ƙasar suna birnin Abuja inda ake taron ƙaddamar da littafin tarihin tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.

Bikin wanda ya samu halartar tsoffin shugabannin Najeriya da suka haɗa da Janar Yakubu Gowon da janar Olusegun Obasanjo da Abdussalami Abubakar da kuma tsoffin shugabannin ƙasar Ghana, Nana Akufo Addo da na Sierra Leone Arnest.

Littafin mai shafi fiye da 400 da janar Babangida ya rubuta da hannunsa ya yi waiwaye kan rayuwar tsohon shugaban ƙasar daga yarintarsa a matsayin maraya har zuwa rayuwarsa ta makaranta da aikin soji in da ya zama shugaban ƙasa.

Da yake yinbitar littafin, tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce littafin ya yi cikakken bayani kan juyin mulkin soji da irin rawar da janar Ibrahim Babangidan ya taka.

A karon faro janar Babangida a cikin littafin ya amince da cewa Cif Mashood Abiola shi ne ya ci zaɓen da aka rushe a ranar 12 ga watan Yunin 1993.

“Lallai Mashood Abiola shi ne ya lashe zaɓen shugaban ƙasa a 1993 bayan da ya samu ƙuri’u fiye da miliyan takwas inda ya samu nasara a kan Bashir Othman Tofa na jam’iyyar NRC mai ƙuri’a fiye da miliyan biyar.” In ji Janar Babangida a cikin littafin da ya rubuta da kansa.

Abdulsamad Isiyaka Rabi’u shugaban rukunin kamfanonin BUA da Janar Theoplus Ɗanjuma wanda aka wakilta suka jagoranci ƙaddamar da littafin da ɗakin karatu.

Yayin da Abdussamad ya bayar da kyautar naira biliyan biyar ga ginin ɗakin karatun, shi kuma janar Ɗanjuma ya sanar da bayar da naira biliyan uku, inda shi kuma Alhaji Aliko Ɗangote ya sanar da naira biliyan takwas.

Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Godswill Akpabio ya bayar da naira miliyan 50 inda shi kuma mataimakin shugaban majalisar ya sanar da naira miliyan 20.

BBC

Domin samun sauran shirye-shiryen  Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibiyarmu a 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *