Ambaliya Ta Lalata Gidaje Sama Da 60 A Nasarawa

FB IMG 1696113132565

Akalla gidaje 60 da kayayyaki na miliyoyin Nairori suka salwanta sakamakon wata ambaliya da ta mamaye Ƙananan Hukumomin Jihar Nasarawa guda biyu.

Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar, Zachary Allumaga, ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Lafiya, babban birnin Jihar ranar Asabar.

Ya ce an samu ambaliyar ce a Kananan Hukumomin Lafiya da Toto a watan Agusta, kuma ta raba mutane da dama da muhallansu sannan dukiyoyi suka salwanta.

A cewar shugaban, a Lafiya, an samu ambaliyar ce a unguwar da galibi daliban Jami’ar Tarayya da ke Lafiya ne suke zama a cikinta.

Zachary ya ce ta lalata kwamfutoci da katifu da littattafai da kayan abinci da sauran kayayyaki.

A Karamar Hukumar Toto kuwa, ya ce ambaliyar ta lalata sama da gidaje 60.

Ya ce ambaliyar ta Toto ta samu ne sakamakon zaizayar kasa.

Shugaban ya ce tuni hukumar ta fata shirye-shiryen raba kayan tallafi ga mutanen da ambaliyar ta shafa.

Aminiya

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai  👇

https://chat.whatsapp.com/FNim39ly65N2CzcTt8FgWb

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *