Ambaliyar Ruwa Ta Kashe Mutane Uku Da Lalata Dukiya Ta Miliyoyin Naira A Kebbi

Biyo bayan mamakon ruwan sama da aka shafe sa’o’i da dama a ranar Asabar a unguwar Dakingari da ke karamar hukumar Zuru a jihar Kebbi, an tabbatar da mutuwar mutane uku.

Alfijir Labarai ta rawaito Shugaban karamar hukumar Suru, Alhaji Muhammad Lawal Suru, ya ce baya ga mutuwar mutane uku, ambaliyar ta kuma lalata dukiyoyi na miliyoyin naira.

Ya ce bayan ruwan sama kamar da bakin kwarya, ruwan da ke gangarowa daga tsaunukan da ke kewayen garin Dakingari ya taimaka wajen ambaliyar.

Ya ƙara da cewa, “Sama da shekaru ashirin muna fama da ambaliyar ruwa lokacin da damuna take sauka.

Gwamnatocin baya na Nasamu Dakingari da Atiku Bagudu sun gina magudanan ruwa a garin domin magance matsalar amma hakan bai hana faruwar ambaliyar a duk shekara ba.”

A cewarsa, za a iya hana ambaliya idan za a iya gina shinge da Kwalabati a kewayen tsaunukan.

Ya yi kira ga al’ummar yankin da su daina yin gine-gine a magudanar ruwa, da kuma zubar da shara ba gaira ba dalili.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@musa_bestseller

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/Jmw5CBsPV6H3DbSgnlFUHM

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *