A yayin da watan azumin watan Ramadan ke cigaba da gabatowa, masu bukata ta musamman sun bayyana bukatarsu ga Gwamnatin Kano ta tsoma su cikin shirye shiryen ta.
A ganawar sa da Jaridar Alfijir Labarai…. Shugaban hadakar kungiyar masu bukata ta musamman Abdul Haruna ya nemi hadin kan Gwamna Yusuf kan ayyukan da ke inganta haÉ—a kai da kuma cigaban rayuwar al’ummar Jihar kano.
…. Ya jaddada cewa wasu lokuta masu bukata ta musamman na fuskantar koma baya wajan samun ingantattun ababen more rayuwa la’akari da gabatowar watan azumi da suka hadar da kayan bukatun yau da kullun, abinci da kayan masarufi, a lokacin azumin Ramadan.
Kungiyar ta bukaci Gwamna Yusuf da ya yi la’akari da yadda ake ware kayan ciyarwa lokacin azumi a shirye-shiryen gwamnati da ke gudana tare da masu bukata ta musamman da nufin samar da abinci, kayan masarufi, magunguna, da kuma karfafa tattalin arzikin su ta hanyar tallafi a fadin kananan hukumomi 44 na jihar Kano.
A cewar Abdul, babu shakka shirin zai taimaka wajan inganta zamantakewar al’umma da inganta walwalar masu bukata ta musamman a lokacin azumi.
Hakanan, Tawagar ta nemi taimakon Gwamnati wajan shigar dasu tsarin auren Gata da akesaran gabatarwa bayan sallah ga wadanda suka cancanta. “Wannan shiri tabbas ko shakka babu zai inganta zamantakewa, daidaiton jinsi, da yancin masu bukata ta musamman don shiga kowanne fanni na rayuwa”
Acewar Haruna ta hanyar baiwa matasa masu bukata ta musamman damar yin aure, da basu dama a shirye shiryen Gwamnati ne hakan zai cire duk wani shinge wanda galibi ke mayar da su saniyar ware a mafi akasarin tsare tsaren Gwamnatin na tallafa wa al’umma da kuma amincewa da hakkokinsu na rayuwa.
Ana hasashen cewa daurin auren Gata zai yi tasiri matuka wajan inganta rayuwar masu bukata ta musamman, da inganta hadi kan jama’ar su, da kuma amincewa da ‘yancinsu na al’umma.
A baya dai an aiwatar da makamancin wadannan tsare-tsare, irinsu bikin auren gata na Kano, da nufin magance matsalolin zamantakewa, da suka hada da sauke nauyin kudin aure ga iyaye.
A cewar shugaban tare da goyon bayan gwamnati ne kawai, masu bukata ta musamman a jihar Kano za su iya shiga a dama dasu wajan samar da yanayi mai ma’ana.
A yayin da Watan Azumin Ramadan ke cigaba da gabatowa, akwai bukatar mai da hankali wajan tallafawa jama’a don jin dadin dukkan ‘yan kasa, gami da masu bukata ta musamman.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news Za ju iya bibiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/IqPyC2oGzdQ9NudcMXFqHZ