Ana zargin ‘yan Najeriyar 2; Samuel da Samson Ogoshi da gudanar da wata kungiyar zambar-lalata ta kasa da kasa daga Najeriya ta hanyar gabatar da kansu
Alfijir Labarai ta rawaito an daure ‘yan Najeriyar 2, yaya da kani mai shekaru 17 da rabi a gidan kaso bayan da suka amsa laifin yin yaudara ta hanyar lalata a intanet da matasa maza a fadin Amurka.
Wadanda suka zambatar sun hada da wani matashi dan shekara 17, Jordan Demay, daga jihar Michigan wanda ya hallaka kan sa da kan sa.
A ranar Alhamis, wani alkalin kotun tarayya ya yankewa Samuel Ogoshi mai shekaru 24 da kaninsa Samson Ogoshi dan shekara 21 hukunci bayan da ya saurari bayanai masu ban tausayi daga iyaye da matar uban Jordan Demay.
Ana zargin ‘yan Najeriyar 2; Samuel da Samson Ogoshi da gudanar da wata kungiyar zambar-lalata ta kasa da kasa daga Najeriya ta hanyar gabatar da kansu a matsayin mata tare da zambatar wadanda suka fada hannunsu su aiko musu da hotunansu na batsa.
Bayanai sun nuna Samuel Ogoshi ya yi amfani da shafin sada zumunta mai suna dani.robertts a ranar 25 ga watan Maris 2022, bayan da suka rudi DeMay ya tura masu hotonshi tsirara, sannan ya yi masa barazana don ya biya toshiya.
A hirar ta da tashar talabijin ta TV6 mahaifiyar DeMay ta ce bata taba yin tsammanin hukumomi za su iya kamowa da kuma hukumta wadanda su ka yi sanadin mutuwar danta ba, ta ce, hukumomi sun yi daidai da suka tasa keyarsu zuwa Amurka domin amsa laifinsu.
VOA
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj